A yau asabar 18 ga watan Maris 2023 ne ake gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a fadin kasar nan.
Za a gudanar da zaben Gwamna a Jihohi 28 a fadin kasar inda wasu Gwamnonin da ke kan karagar mulki ke neman sake tsayawa takara yayin da akasarin Jihohin za su zabi sabbin shugabannin zartaswa.
A Legas, Babajide Sanwo-Olu na neman sake tsayawa takara a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayin da jam’iyyar PDP ta tsayar da Abdul-Azeez Olajide Adediran a matsayin dan takararsu, kuma za su fafata da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam’iyyar Labour. .
Manyan jam’iyyun siyasa biyu, PDP da APC ne suka fi yawan ‘yan takara a zaben na ranar Asabar amma sai sun kara yin aiki don samun nasara a wasu jihohin da jam’iyyar Labour ke da ‘yan takara.
A Akwa Ibom, Akan Udofia ne dan takarar jam’iyyar APC, sauran jihohin kuma sun hada da: Abia – Ikechi Emenike, Adamawa – Aishatu Dairu Binani , Bauchi – Sadique Abubakar, Kaduna – Uba Sani, Gombe – Muhammadu Inuwa Yahaya, Delta – Ovie Omo-Agege, Borno – Babagana Zulum, Cross River – Bassey Otu, Jigawa – Umar Namadi, Kano – Nasiru Yusuf Gawuna, Ebonyi – Ogbonna Nwifuru, Enugu – Uche Nnaji, Katsina – Dikko Umaru Radda, Kebbi – Nasiru Idris, Kwara –AbdulRahman AbdulRazaq, Ogun – Dapo Abiodun, Nasarawa – Abdullahi Sule, Plateau –Netanwe Yilwatda, Rivers – Tonye Cole, Yobe –Mala Buni, Zamfara – Muhammad Bello, and Oyo – Teslim Folarin
‘Yan takarar PDP a fadin kasar nan sune Eleazar Ikonne – Abia., Umaru Fintiri – Adamawa., Umo Bassey – Akwa Ibom., Ibrahim Mohammed – Bauchi., Titus Uba – Benue, Mohammed Ali Jafari – Borno, Sheriff Oborevwori – Delta, Peter Mbah. – Enugu, Muhammad Barde – Gombe, Mustapha Sule-Lamido – Jigawa, Isa Ashiru Kudan – Kaduna, Muhammed Abacha – Kano., Aminu Bande – Kebbi.,Abdullah Yahman – Kwara, Abdul-Azeez Adediran – Lagos. David Ombugadu – Nassarawa, Segun Sowunmi – Ogun, Seyi Makinde – Oyo, Caleb Mutfwang – Plateau, Siminialayi Fubara – Rivers, Sa’adu Umar – Sokoto
Kefas Agbu – Taraba, Sheriff Abdullahi Yobe, Dauda Lawal – Zamfara.
Jam’iyyar Labour ta bai wa jam’iyyun siyasa da suka dade da kafa damar samun kudadensu a zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu kuma ana jin cewa batun Peter Obi na iya sake mamaye kasar a yau.
Ku biyo mu don jin karin bayani, sakamakon zaben gwamna a jihohi 28.