Tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa na amfani da tsohuwar takardar naira wajen sayen kuri’u a jihar Kaduna.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren ranar Asabar, tsohon dan takarar gwamna a jihar Kaduna, ya ce ana biyan mutane Naira 1000 zuwa N2000 don zaben wata jam’iyya.
Ya rubuta cewa, “Tsoffin takardun Naira da kotun koli ta yi wa doka ta zama makamin sayen kuri’u a jihar Kaduna.
“Mutane, akasari mata matalauta a cikin birni da kuma bayan an biya su daga 1k zuwa 2k don kuri’unsu.”
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na daya daga cikin gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC da suka kai gwamnatin tarayya gaban kotun koli, inda suka bukaci a dawo musu da tsofaffin takardun kudi.