Terem Moffi da Calvin Bassey da kuma Victor Sochima sun isa sansanin ‘yan wasan Super Eagles na John Woods da ke Abuja.
Zuwan ‘yan wasan uku ya kara yawan ‘yan wasan da ke sansanin zuwa 18.
Ana sa ran ‘yan wasa biyar da suka hada da dan wasan gaba na Napoli da Victor Osimhen da kuma mai tsaron bayan Porto Zaidu Sanusi a sansanin
Ana sa ran kungiyar za ta hada kai da abokan wasan gabanin atisayen da za a yi ranar Talata (yau) a filin wasa na Moshood Abiola, Abuja.
Taron horon wanda zai dauki tsawon awa daya, zai fara ne da karfe 7 na yamma.
Mintuna 15 na farko na zaman ne kawai za su kasance a buɗe ga manema labarai.